Bayani game da WhatsApp Business Course
Mutane da yawa na amfani da Manhajar WhatsApp Business amma ba yanda ya kamata ba. Ita WhatsApp Buisiness tana taimaka wa ‘yan kasuwa, musamman kanana da matsakaita, wajen sauƙaƙe sadarwa da abokan ciniki. Tana ba su damar ƙirƙirar bayanan kasuwanci da ke ƙunshe da suna, adireshi, lokaci na aiki, da bayanin kayan aiki ko ayyuka. Hakanan tana ba da damar aika saƙonni cikin sauri ta hanyar amsoshi na atomatik da sakonni na maraba. WhatsApp Business na amfani da alamu don tsara abokan ciniki gwargwadon bukatu, da kuma daura advert saboda samun kasuwa. Ta haka, ‘yan kasuwa za su iya bauta wa abokan huldarsu cikin sauri da inganci, su kuma gina amincewa, wanda zai taimaka wajen haɓaka kasuwa da samun ci gaba.
Za a bayar da certificate (shaidar course)?
A ƙarshen wannan kwas, za a ba da shaidar kammalawa daga Arewa Digital Academy.
Masu Amfana da Kwas na WhatsApp Business da Yadda Za Su Yi Amfani da Shi:
- An tsara kwas na WhatsApp Business domin wadannan masu amfana:
- Kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa – domin su inganta sadarwa da abokan ciniki, kara bayyana kasuwancinsu, da bunkasa tallace-tallace ta WhatsApp.
- Masu farawa da sabbin ‘yan kasuwa (entrepreneurs) – domin su koyi amfani da WhatsApp Business a matsayin kayan aiki mai sauki da arha wajen talla da hidimar abokan ciniki.
- Masu aikin talla ta yanar gizo (digital marketers) – don kara fasaha wajen tsara dabarun sadarwar kasuwanci.
- Ma’aikatan kula da abokan ciniki – don su inganta mu’amala da abokan ciniki ta hanyar fasalolin WhatsApp.
- Dalibai da masu neman aiki – masu sha’awar koyon dabarun kasuwanci na zamani don samun aiki ko yin aikin kansu.
Course Availability
The course is available for up to 16 weeks from date of purchase
Curriculum
- 3 Sections
- 19 Lessons
- 16 Weeks
- Gabatarwa da Amfanin WhatsApp Business (Introduction and Usefulness of WhatsApp Business)4
- 1.1Lesson 1: Course Outline- Jerin abubuwan da za a koya a cikin kwas2 Minutes
- 1.2Lesson 2: Benefits of WhatsApp Business (Amfanin WhatsApp Business)7 Minutes
- 1.3Lesson 3: Downloading and Getting Started (Saukar da Manhajar da farawa)4 Minutes
- 1.4Lesson 4: General Setting up of WhatsApp Business (yanda ake seta profile)10 Minutes
- Kasuwanci da WhatsApp Business (Business Tools)8
- 2.1Lesson 5: Customer settings (Labels and payments settings)5 Minutes
- 2.2Lesson 6: Sending automatic message (Aika sakonin ko ba ka online)10 Minutes
- 2.3Lesson 7: Create catalogue (kirkira catalogue na tallata abubuwan sayarwa)8 Minutes
- 2.4Lesson 8: Amfani da Broadcast da Business Groups7 Minutes
- 2.5Lesson 9: Jawo hankalin customers zuwa gareka11 Minutes
- 2.6Lesson 10: Talla (advertising) a cikin WhatsApp8 Minutes
- 2.7Lesson 11: Linking WhatsApp Business da Instagram da Facebook4 Minutes
- 2.8Lesson 12: Amfani da “WA.Link” domin sharing da mabiya da customers8 Minutes
- Fa'idodin fasalolin WhatsApp Business7
- 3.1Lesson 13: Amfani da “WhatsApp Poll” domin jin ra’ayoyin customers5 Minutes
- 3.2Lesson 14: Security a WhatsApp Business (2-Step verification)4 Minutes
- 3.3Lesson 15: Gane yawan sakonin da yawan status views4 Minutes
- 3.4Lesson 16: Privacy, blocking da disappearing messages4 Minutes
- 3.5Lesson 17: Yanda ake chatting da sabobin clients da customers2 Minutes
- 3.6Lesson 18: Kare account dinku daga hackers ko scammers10 Minutes
- 3.7Lesson 19: Kammala Course, da samun “Certificate”5 Minutes
Requirements
- Basic knowledge of mobile device (Android or iOS)
Features
- Learn unknown features of WhatsApp Business and how to exploit it for new markets/audiences
Target audiences
- Business owners; online marketers; social media managers; companies and corporate organisation